An Gano Tulin Muggan Makamai A Jos Babban Birnin Jihar Filato

IMG 20240308 WA0095

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gano makamai masu yawa na zamani da kuma ?irar gida a gundumar Fann da ke yankin ?aramar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato.

Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce sun ?addamar da samame a ?auyukan gundumar ne bayan da wasu ?ata-gari suka kashe wani jami’in shige da fice a lokacin da jami’an tsaro ?ar?ashin rundunar Operation SAFE HAVEN ke sintiri a yankin.

An ce ?ata-garin sun kashe jami’in a lokacin da yake duba motarsu wadda aka yi zargin sun ?auko makamai a cikinta.

Bayan haka ne jami’an sojojin suka ?addamar da samame da nufin gano makamai tare da kama mutanen da ake zargi da hannu a lamarin.

”Bayan shafe mako guda, dakarunmu sun kama mutum takwas tare da gano makamai na zamani da kirar gida a ?auyukan Ratas da Ratoso da kuma Sangasa duka a gundumar Fann da ke yankin ?aramar hukumar Barikin Ladi”, in ji sanarwar.

Makaman da aka gano a lokacin samamen sun ha?a da:

Bindiga ?irar AK-47, 12 da samufurin AK-47 ?irar gida 12, da ?anannan bindigogi 15 da kwanson harsasan AK-47 15 da kakin soja, da harsasai 250 da sauran makamai da kwari da baka da babura bakwai.

Related posts

Leave a Comment