Wani bidiyo da ya karade kafafun sadarwa a jiya ya nuna yadda aka gano gawarwakin wasu mutane shida a wani rafi dake kusa da gidan tsohon kakakin majalisar tarayya, Honarabul Yakubu Dogara.
Idan ba a manta ba dai, a makon da ya gabata ne wasu matasa suka fasa gidan Honarabul Dogara dake garin Jos suka kwashi kayayyaki a lokacin da wasu talakawa ke fasa rumbunan abinci a sassan jihohin nan suna kwashewa da sunan tallafin corona da aka jibge aka ki ba su.
Saidai rahotanni sun nuna cewa bayan kwana biyu an yi ta tsamo gawarwakin mutane a rafin da yake kusa da gidan na Dogara bayan da sojoji suka tarwatsa masu fasa gidan da harbi, wanda hakan ya sanya wasu suka fada rafin don gudun ceton rai.
Zanga-Zangar Endsars ne ta zama wata annoba a Najeriya, lamarin da ya sanya Gwamnoni da sauran shugabannin tsaro da Sarakuna, ?aukar matakan zaman gaggawa domin shawo kan matsalar.