An gabatar da kudirin dokar yin gyara ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ?ananan hukumomin jihar Sokoto a gaban majalisar dokokin jihar a jiya Talata.
?udurin dai ya janyo ce-ce-kui-ce, kasancewar ana ganin idan aka amince da dokar za ta rage ?arfin iko na mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III.
Bayan gabatar da ?udurin a zauren majalisar, nan take aka yi masa karatu na farko da na biyu, sannan aka mi?a shi ga kwamitin da ke lura da ?ananan hukumomi da masarautu.
An bai wa kwamitin kwana 10 domin tattaunwa tare da gabatar da rahoto a zauren Majalisar.
Idan aka amince da dokar, za ta soke gyaran da aka yi na shekara ta 2008, wadda ta bai wa sarkin Musulmi damar na?a hakimai da iyayen ?asa kai tsaye.
Hakan na nufin sarkin Musulmin ba zai iya na?a irin wa?annan mu?amai ba har sai ya samu sahhalewar gwamnan jihar, kamar yadda ake yi gabanin shekarar ta 2008.
A kwanakin baya ne gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya sauke wasu daga cikin hakiman da masu ri?e da masarautun gargajiya da ke jihar.