An Fara Gwanjon Gwala-Gwalan Tsohuwar Ministar Mai

Kwamitin da aka kafa domin sayar da kayayyakin da gwamnatin tarayya ta kwace daga masu laifi ta fara sayar da wasu kadarori 25 a sassan kasar daban-daban.

Mista Daya Apata, Shugaban kwamitin ya sanar da hakan a jiya yayin taron manema labarai a birnin Tarayya Abuja.

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari a ranar 9 ga watan Nuwamba na shekarar bara ya kafa kwamitin bayan ganin akwai bukatar hakan sannan ya umurci ofishin Ministan Shari’a na kasa ya saka ido kan ayyukan kwamitin na karbo kadarorin gwamnati da sayar da su.

Mista Apata ya ce kwato kadarorin gwamnati da sayar da su na cikin ayyukan shari’a. Ya ce kwamitin yana da wakilai daga hukumomin tsaro da suka hada da, Yan sanda, Sojojin Ruwa, EFCC, ICPC da ma’aikatun kudi, shari’a, ayyuka da sauransu.

Cikin kadarorin da za a sayar akwai filaye, masana’antu, injina, motoccin hawa, kayan ado kamar gwala-gwalai da sauransu.

Duk da cewa sanarwar ba ta fayyace kadarorin da za ayi gwanjon su ba, EFCC a baya ta samu izini daga kotu na fara sayar da wasu kadarorin da ta kwace daga hannun tsohuwar ministan man fetur, Alison Diezani Madueke.

Kotun tarayya a Legas ta bada umurnin kwace gwala-gwalai na Diezani da kudinsu ya kai Dalla miliyan 40. Duk dai a shekarar, kotu ta kwace kimanin Naira biliyan 12.2 mallakar Patience Jonathan tsohuwar matar shugaban kasa Goodluck Jonathan.

An kuma kwace wani asibiti (Dews Hope Hospital, a Owerri) na N1.5 biliyan da aka alakanta da hadimin tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

Bayan taron, kwamitin ya ziyarci wasu wurare hudu a Abuja ciki har da gida mai lamba 14 Adzope Crescent Wuse 2 Abuja da aka kwace daga tsohon babban hafson sojojin sama daga bisani babban hafson tsaro, Alex Badeh.

Related posts

Leave a Comment