An Cire Bambancin HND Da Digiri A Hukumomin Tsaron Najeriya

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta cire banbancin matsayi da karin girma da ke tsakanin masu takardar karatu ta babbar Diploma HND da kuma Digiri, a hukumar tsare ta Civil Defence, Hukumar Shige da Fice, Hukumar kula da gidajen yari da kuma hukumar Kashe Gobara da ke karkashin ma’aikatar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar cikin gida mai dauke da kwanan watan ranar 16 ga watan Oktoba, wadda sakataren hukumomin Alhassan Yakmut ya sanya wa hannu kuma aka gabatar a karshen taron hukumar gudanarwar ma’aikatar.

Sanarwar, ta ce daga yanzu, dukkan jami’an da aka dauka da kwalin HND, za a ba shi matsayin mataimakin Supretendant na biyu da matakin albashi na 8, kuma zai ci gaba da samun karin girma ba tare da nuna banbanci ba.

Ku kasance damu a shafin mu na www.muryarysnci.com domin samun ingantattun labarai da dumi duminsu

Related posts

Leave a Comment