An Cimma Yarjejeniyar Zaman Fulani A Jihohin Yarbawa

Gwamnonin kudu maso yammaci da na arewacin Najeriya sun cimma yarjejeniya game da zaman Fulani a yankin ƙabilar Yarbawa.

Taron wanda shi ne irinsa na farko tun wa’adin kora da aka ba Fulani su fice daga yankin jihohin Ondo da Oyo ana ganin ya samu nasara sakamakon amincewar da gwamnonin da Fulani makiyaya suka yi kan sha’anin kiwo a gandun dazuzzuka a yankin na Yarbawa.

Ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya ne a taron da suka yi da ƙungiyar gwamnoni a Akure a Litinin.

Kuma sun amince da buƙatu 13 da suka haɗa da hana kiyo cikin dare da mamaye dazukan gwamnati da kuma ƙayyade shekarun kiwo.

Kuma dole kungiyar Fulani makiyaya ta rungumi tsarin kiyo na zamani ta hanyar samar da matsuguni ga mambobinta tare da hana su yawo.

An yi taron ne da gwamnonin arewa da suka ƙunshi na Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da Jigawa Badaru Abubakar da kuma takwarorinsu na Oyo da Rotimi Akeredolu na Ondo da Ekiti Kayode Fayemi da Osun Gboyega Oyetola na yankin kudu maso yamma da nufin wani yunƙuri na lalubo bakin zaren warware zaman ɗar-ɗar da ake yi.

Gwamnan Ondo ya ce kafofin yaɗa labarai sun yi wa umurnin da gwamnatinsa ta bayar muguwar fahimta inda ya ce ya bayar da umurni ne kawai ga makiyaya su fice da suka mamaye daji ba bisa ka’ida ba.

Kuma sun yarda cewa matsalar tsaro ƙalubale ne da ya shafi ƙasa ba wata ƙabila ba ko wani yanki.

Wannan ganawa ta kasance irin ta farko, wadda ta mayar da hankali wajen yin sulhu tsakanin makiyaya da kabilar Yarbawa sakamakon zargin da ake yi cewa makiyayan suna haddasa matsalar tsaro a jihohin da ke yankin.

Kuma taron ya kunshi shugabannin Fulani makiyaya a Najeriya.

Ce-ce-ku-ce tsakanin bangarorin biyu ya ta’azzara ne bayan gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bai wa makiyaya wa’adin mako guda su fice daga dazukan jihar.

Gwamna Akeredolu ya yi zargin cewa makiyaya ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.

“A yau mun dauki manyan matakai na warware matsalolin satar mutane a hannu daya, da kuma sauran miyagun laifuka wadanda rahotanni kan tsaro da ‘yan jarida da kuma wadanda lamarin ya rutsa da su a jihar Ondo suka yi ciakken bayani a kansu,” in ji gwamnan.

A cewarsa: “Galibin wadannan matsaloli ana danganta su da wasu bara-gurbi da ke fakewa da sunan makiyaya . Wadannan masu aikata laifuka sun mayar da dazukanmu a matsayin wuraren da suke boye mutanen da aka sace, inda suke tattaunawa domin karbar kudin fansa sannan su aikata wasu laifukan.”

Kazalika wani dan bangar Yarbawa Sunday Igboho ya dora alhakin matsalolin tsaron da ke faruwa a yankin kan makiyaya inda ya umarce su su bar yankin.

Sai dai makiyayan sun musanta wannan zargi suna masu cewa kora-da-hali yarbawa suke yi musu.

Shi ma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnan jihar ta Ondo kan matakin korar makiyaya daga dazukan jihar yana mai yin kira ga bangarorin biyu su hau teburin zaman lafiya.

“Babu wani abin cewa illa kira ga ɓangarorin su yi sulhu da kuma neman gwamnatin jihar da kuma shugabancin Fulani su ci gaba da tattaunawa domin fahimtar juna domin kawo ƙarshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihar cikin sauri,” in ji shugaban.

Daga bisani kakakin shugaban kasar malam Garba Shehu ya shaida wa BBC Hausa cewa za su sanya kafar wando daya da duk gwamnan da ya kori makiyaya daga jiharsa domin kuwa kudin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa dukkan ‘yan kasar damar zama a duk inda suke so.

Kan wannan batu manyan mutane daga sassan kasar daban-daban sun ta tofa albarkacin bakinsu, suna cewa idan ba a dauki matakin da ya dace ba Najeriya za ta iya fadawa yakin basasa.

Cikin wadanda suka yi magana har da tsohon shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki, wanda ya nemi shugaban kasar Muhammadu Buhari ya shirya taron masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Daga kudancin kasar basaraken kasar Ibadan Oba Saliu Adetunji, ya yi gargadin cewa dora alhakin matsalar tsaron kasar kan wata kabila zai iya haifar da tashin hankali.

Babu shakka sanarwar tattaunawar za ta yi wa mutane da dama a kasar dadi, domin kuwa tamkar wani mataki ne na yayyafawa wutar rikicin da ke ruruwa tsakanin bangarorin biyu ruwa.

A makon da ya gabata wani da ke kiran kansa jagoran matasan Yarbawa wato Sunday Igboho ya bai wa Fulanin wa’adin su fice daga jihar Oyo cikin kwanaki bakwai.

Bayan nan sai Gwamnan Ondo ya fitar da sanarwar cewa makiyaya su fice daga dazukan jiharsa.

Kudancin Najeriya dai na da korayen dazukan da Fulani ke zuwa kiwo tun a baya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply