An Ceto Yaran Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Jihar Katsina

An sace yaran ne a ranar Lahadi yayin da suke aiki a wata gona a garin Mairuwa, dake yankin ƙaramar hukimar Faskari dake Jíhar.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Sambo Isah ya tabbatar da sakinsu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Ya ce wadanda aka ceto din sun hada da mata 17 da maza hudu kuma tuni an sada su da yan uwansu yayin da ake cigaba da bincike. Sanarwar ta ce:

“Barka da yamma yan jarida. Ina farin cikin sanar da sakin ma’aikata 21 da aka sace a gona a kauyen Kamfanin Mai Lafiya jihar Katsina. An sada su da yan uwansu. Ana kuma cigaba da bincike.”

Kakakin yan sandan bai fadi ko an biya kudin fansa ba ko ba a biya ba, A gefe guda, wata majiya daga garin wadanda aka sace din ta shaidawa wakilinmu cewa yan ta’addan suna neman a biya su fansar Naira miliyan 30 ko basu daman yin magana kai tsaye da mai gonar da wadanda aka sace suke aiki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply