Wani jaki ya shaƙi iskar ƴanci bayan da dakarun rundunar ƴan sanda suka kuɓutar da shi da ga hannun ƴan fashin dajin da su ka yi garkuwa da shi a Jihar Katsina.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, Kakakin rundunar ƴan sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da kuɓutar da jakin, tare da sauran dabbobin gida da dama, a yayin da ya ke bayanin irin nasarar da rundunar ta samu a shekarar 2021 ga manema labarai a Katsina.
A cewar SP Isah, rundunar ta ƙwato dabbobi 1, 243, inda yai bayanin cewa 867 da ga ciki shanu ne, tumaki 352, awaki 24 sai kuma shi wannan jaki guda 1.
Sannan SP Isah ya yi bayanin cewa ƴan ta’addan na amfani da jaki ne gurin tafiye-tafiye ko yin hijira zuwa dazuka, in da ya ce su na ɗora masa kaya, ƴaƴansu da ma matan su a kai wajen yin bulaguro.
Ya ƙara da cewa jakin na mutanen gari ne, sai su ƴan fashin dajin, idan sun zo satar dabbobi, sai su haɗa da jakuna domin su na amfani dasu.
Sun kama masu laifi har 999 a shekarar da ta gabata a jihar, sannan sun kama bindigogi da alburusai da dama.
Kakakin ya yi wa mutanen Katsina, da ma na ƙasa baki ɗaya albishir cewa a na sa ran a shekarar 2022 ɗin nan, mutanen Katsina da maƙwabtanta za su ga ingancin tsaro sosai in Allah Ya yarda.
Ya ce gwamnatin taraiya za ta samar da sabbin kayan aiki, gami da ɗaukar sabbin jami’an ƴan sanda, da kuma amfani da hanyoyin fasaha ta yaƙi da ƴan ta’adda, da dai sauransu.