Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ta kai samame gidan wasu batagari da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Kano. A cewar rundunar, jami’anta sun samu nasarar cafke mutane hudu gidan, cikinsu har da wata mace.
Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya ce an kama mutanen yayin samamen da jami’an tsaro suka kai gidan da ke kauye Jaba, karamar hukumar Ungogo.
A cewar kakakin, binciken rundunar ‘yan sanda ya gano cewa matar da aka kama ce ta karbi hayar gidan ta hannun wani dillali a unguwar.
Matar ta karbi hayar gidan ne akan dubu dari shidda (N600,000) a shekara, a cewar DSP Kiyawa.
DSP Kiyawa ya kara da cewa matar ta shiga kasuwancin garkuwa da mutane bayan an kashe mijinta wanda shi kansa yana cikin ‘yan bindiga da ke satar shanu a jihar Zamfara.
A watan Oktoba na shekarar 2020 ne rahotanni suka bayyana cewa an yi garkuwa da akalla yara tara a jihar Kano.
Kazalika, an sace Aishatu Aliyu, matar dagacin garin Tsara, Aliyu Muhammad, a cikin watan Oktobar.
A cikin watan Nuwamba ne kuma kafafen yada labarai suka sanar da cewa masu garkuwa da mutane sun sace Babawuro Tofai, kanin ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono.