Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wani tsoho dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram miyagun kwayoyi.
Hukumar NDLEA ta ce tsohon na zuwa ne daga jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar inda daga nan yake shigo da kwayoyin cikin kasar ta Najeriya.
Cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce, tsohon mai suna Muhammad Rabi’u Wada da ke kai wa Boko Haram da ‘yan bindiga kwaya an kame shi ne a jihar Neja kan hanyarsa ta komawa Jamhuriyar Nijar.
A wani samame da hukumar ta kai mai kama da wannan, ta samu nasarar lalata gonar tabar wiwi a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya wadda girmanta ya kai kimanin hekta 95.
An samu gonar ne a wani dajin dake Ogbese, sai dai ba a samu nasarar kame kowa ba yayin samamen, amma ana ci gaba da bincike domin gano wanda ya mallaki gonar.
A jihar Kogi da ke arewacin kasar ta Najeriya, har ila yau Hukumar ta samu nasarar kwace tabar wiwi da ta kai kimanin kilogiram 116.1 a wani shingen ababan hawa a yankin Okene-Lokoja.
Mutumin da aka kama da kayan mai suna Sulaiman Said ya ce ya dauko tabar ta wiwi din ne daga jihar Edo a kudancin Najeriya kuma zai cilla da ita har zuwa Jihar Kaduna ne.