Wani kwararre a fannin tsaro mazaunin Birnin tarayya Abuja Dr. Sani Aliyu ya yi kira da babbar murya ga Shugaban ?asa da ya yi gaggawar sallamar mai bashi shawara akan tsaro nan take ba tare da ?ata lokaci ba.
Dr. Sani ya yi wannan kiran ne a yayin wata tattaunawa da Gidan talabijin na Liberty ya yi dashi cikin wani shiri na musamman, inda yace shika-shikan sallamar Janar Monguno sun wajaba ta la’akari da yadda ya gaza wajen sauke nauyin da aka aza mishi na daidaita harkar tsaro a kasar.
” Idan muka duba yadda mai bada shawara ya fadi warwasa wajen gudanar da aikinsa, da yadda harkar tsaro ta ?ara ta?ar?arewa a ?ar?ashin jagorancin shi, manyan dalilai ne da suka wajabta Shugaban ?asa ya sallame shi”.
Dr. Sani Aliyu ya yaba gami da yin jinjina ga Shugaban ?asa Buhari na amsa kiran ‘yan Najeriya wajen sallamar shugabannin tsaro, amma hakan zai zamana kamar an kashe Maciji ne ba a sare kanshi ba, muddin aka bar Munguno akan mu?amin shi na mai bada shawara ba tare da sallamar shi ba.
Dr. Sani Aliyu ya kuma soki lamirin wadanda suke kitsa kutungwilar tarwatsa Najeriya ta hanyar cusa gaba ta bangaranci da addini, ta fakewa da rikicin Makiyaya domin haddasa fitina a Najeriya, inda ya bayyana ba za su samu nasara ba, domin Najeriya za ta cigaba da kasancew a matsayin dunkulalliyar kasa da yardar Allah.