An Bankado Yadda Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya Suka Jidi Naira Tiriliyan 13.95 Ba Bisa Ka’ida Ba

IMG 20240308 WA0066

Aƙalla Naira tiriliyan 13.95 ne Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati suka jida ba bisa ƙa’idar da Kundin Dokokin Najeriya ya shar’anta ba.

Rahoton da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya fitar ne kan yadda hukumomin gwamnati suka kashe kuɗaɗe a shekarar 2020.

Rahoton ya fallasa cewa jidar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba ya kawo naƙasu da tawaya wajen kasa tantance daidaiton gano kuɗaɗen da aka fitar aka yi aiki da su har Naira 13,955,069,757,335.00.

Wannan gurungunɗuma dai ta karya Dokar Kuɗaɗen Gwamnati ta 2009, wadda ta ce “Kada gwamnati ta ciri kuɗi daga asusun bankuna kai-tsaye. Idan kuma aka cira, to ma’ajin hukumar ko ma’aikatar zai fuskanci hukuncin biyan kuɗaɗen bankin zai caja.”

Sai dai kuma wata sabalula da asarƙala ita ce an bayyana kuɗaɗen a matsayin aro da ayyukan haƙƙin gwamnati.

Ma’aikatar Muhalli ce aka fi yin wannan karya doka, inda aka jidi Naira biliyan 350.85.

Mai bi mata ita ce Hukumar Binciken Ingancin Abincin da ake Ajiyewa, wato Nigeria Stored Products Research Institute,

Ofishin Biyan Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, wanda ya jide Naira biliyan 27.95.

Benin da Ilorin ne na su adadin da aka jida na su da yawa, kama daga Naira biliyan 107.50 jimlace.

Mai Binciken Kudi na Gwamnatin Tarayya Shaakaa Chira ya ce an jide wadannan kuɗaɗe ba tare da sahalewar gwamnati ba.

Ƙarin abin mamaki kuma shi ne duk ba su yi bayanin ayyukan da aka yi da kuɗin ba.

Chira ya ce karkatar da kuɗaɗen ya faru ne saboda rashin kaƙƙarfar masu sa-ido kan adadin kuɗaɗen da ma’aikatu za su fitar.

Tsarin fitar da kuɗaɗen gwamnatin tarayya ya ƙara da cewa ya gano maƙasudin ƙin bin ƙa’ada wajen cirar kuɗaɗe ne saboda an riƙa watsa wasu kuɗaɗen cikin aljihun masu cirar kuɗaɗen.

Sai dai kuma wata ƙwararriya kan sha’anin bin ƙa’idar cirar kuɗaɗe mai suna Adenike Aloba, ta ce ya kamata a ƙara wa Ofishin Akanta Janar ƙarfi, ba kawai ya tsaya ya na yin kira ko zare ido kaɗai, kaɗai ko cewa a maido da kuɗaɗen da gaggawa kaɗai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply