An ?ara Wa Shugaban ‘Yan Sanda Wa’adin Watanni Uku

Babban Shugaban rundunar ‘Yan Sanda ta kasa Mohammed Adamu, a ranar Alhamis, ya nada babban jami’in sa (PSO), Idowu Owohunwa, da jami’in Ilimi na rundunar, Rabi Umar ado, matsayin kwamishinan ‘yan sanda a hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Hakanan an nada ACP (Dr.) Adegbite Tunde Titus; ACP (Dakta) Chinonyerem Lawrence Welle da kuma Mataimaki na Musamman ga Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Aderoju Olagunju, da sauransu.

Jami’an ‘yan sandan da aka yiwa nadin suna daga cikin sabbin ayyukan hukumar ‘yan sanda da aka daga darajar su, kamar yadda wata sanarwa daga kakakin rundunar ‘yan sanda ta Najeriya @PoliceNG ta bayyana a shafin ta na twitter.

Nadin na daga cikin ayyukan Shugaban ‘Yan Sandan wanda ya ci gaba da aikinsa bayan karin wa’adin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na watanni uku a ranar Alhamis.

Wa’adin Adamu ya cika a ranar Litinin bayan ya kwashe shekaru 35 yana aikin dan sanda. Amma Shugaban kasar ya sanar da kara wa’adin Adamu da watanni uku a ranar Alhamis.

Da yake sanar da hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da Shugaba Buhari, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Muhammad Dingyadi, ya ce shawarar ta bayar da damar zabar wanda zai gaje shi ne ta hanyar da ta dace.

Related posts

Leave a Comment