Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya a shafinta na X ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci sakamako mai ra?a?i.
Amurka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan sace yan makaranta da aka yi a Kaduna da kuma yan gudun hijira a Borno.
Zuciyarmu tana kan iyalan wadanda abin ya shafa. Muna tsayawa tare da ku wajen neman wadanda suka aikata laifin su fuskanci sharia kuma a gaggauta dawo da duk wadanda aka kama.
Muna goyon bayan kokarin Najeriya na ganin an sako su, in ji ta