Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya a shafinta na X ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci sakamako mai raɗaɗi.
“Amurka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan sace ‘yan makaranta da aka yi a Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira a Borno.
“Zuciyarmu tana kan iyalan wadanda abin ya shafa. Muna tsayawa tare da ku wajen neman wadanda suka aikata laifin su fuskanci shari’a kuma a gaggauta dawo da duk wadanda aka kama.
“Muna goyon bayan kokarin Najeriya na ganin an sako su,” in ji ta