Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Koriya Ta Arewa Kan Gwajin Makami Mai Linzami

Koriya Ta Arewa ta yi ikirarin cewa makamai masu linzamin da ta ?addamar ranar Alhamis wasu nau’in “sabbin makaman ne da ake harbawa daga jikin bindiga da nufin ?ara karfin sojinta.”

Koriyan ta fadi hakan ne a wata sanarwa ta farko da ta fitar tun bayan yin gwajin.

Wannan ne karo na farko da ?asar ta harba makaman a cikin kusan shekara ?aya, kuma na farko tun bayan da Joe Biden ya zama shugaban ?asar Amurka.

Mista Biden ya ce Amurka za ta “mayar da martani yadda ya dace”. Amurka da Japan da Koriya Ta Kudu duk sun yi Allah-wadai da gwajin.

A ?ar?ashin ?udurorin da aka cimma na Kwamitin Tsaro na Majalisar ?inkin Duniya, an haramta wa Koriya Ta Arewa gwajin makamai masu linzami.

Sanarwar da ?asar ta fitar a ranar Juma’a da ta fito daga kafar ya?a labaran ?asar KCNA, ta ce makaman biyu na gwajin an harba su ne da nufin yin tafiyar kilomita 600 daga gabashin ga?ar tekun Koriya Ta Arewan, inda bayanin ya ci karo da ?iyasin Japan na cewa sun haura fiye da kilomita 400.

Ya ?ara da cewa sabon makamin yana iya ?aukar abu mai nauyin tan 2.5, wanda zai iya ba shi damar ?aukar kayayyakin makaman ?are dangi.

An ambato Ri Pyong Chol, wani babban jami’i a ?asar wanda aka yi gwajin a gabansa yana cewa: “Samar da wannan tsarin makamin abu ne mai matu?ar muhimmanci ga bun?asar ?arfin sojinmu da da?ile duk wata barazana ta soji.”

Sai dai shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un ba ya wajen lokacin da aka harba makamin.

Tambayar da ake yawan yi ita ce me ya sa Koriya Ta Arewa ke yin gwajin a yanzu?

Babu amsa mai sau?i ta wannan tambaya. Na farko saboda za su iya, kuma Koriya Ta Arewa na da sabbin makaman da za ta gwada.

Amma sa?onnin baya-bayan nan da Koriya Ta Arewa ke garga?in Amurka da ka da ta “tunzura ta” kuma gwamnatin Biden za ta “?an?ana ku?arta” to akwai abin da Arewar ke nufi da hakan.

Hukumar le?en asiri ta Koriya Ta Kudu ta ce ta yi amanna Koriya Ta Arewa ta harba makaman ne a daidai lokacin da Shugaba Biden ke daf da gabatar da taron manema labarai.

Ta kuma yi amannar cewa Arewar ta yi hakan ne don nuna adawa da mi?a ?an ?asarta Mun Chol Myong ga Amurka daga Malaysia, da kuma matakin Hukumar Kare Ha??in Dan adam ta MDD na baya-bayan nan mai adawa da Koriya Ta Arewa.

Ko ma dai mene ne dalilin, sa?on da Koriya Ta Arewa ke aike wa duniya ya sha bambam da wanda take aike wa al’ummarta.

Shafin farko na jaridar ?asar ya nuna Kim Jong-un yana duba sabbin motocin bas-bas na fasinja – ba a ganshi a wajen gwajin makaman ba.

Mista Kim ya na motsa ?wanjinsa ne a idon duniya amma a idon mutanensa yana nuna shi mai kawo musu sauyi ne.

Mr Biden ya shaida wa manema labarai cewa harba makaman keta yarjejeniyar MDD ne, kuma Amurka na tuntu?ar abokan hul?a da ?awayenta.

“Za a mayar da martani – idan har suka sake ta’azzara lamarin, za mu mayar da martani yadda ya dace,” in ji shi.

“Amma kuma a shirye nake ga yin wani abu da ya shafi diflomasiyya amma dole ya kasance akwai shara?i kan lalata makaman nukiliya.

Related posts

Leave a Comment