Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ƙasar Amurka ta ware Dala miliyan 50 domin tallafa wa Najeriya gudanar da zaben shugaban kasa a shekara maai zuwa ta 2023.
Daga cikin abubuwan da za a yi da kudaden har da horas da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula baya ga taimakawa wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da ingantaccen zabe.
Jakadan Amurka, Mista Will Stevens, shi ne ya sanar da tallafin a ranar Litinin a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo a yayin wani taron horas da ‘yan jarida wanda Cibiyar Horas da Yada Labarai ta Yammacin Afrika WABMA ta shirya.
Mista Stevens ya ce, gwamnatin Amurka na aiki tukuru da aminanta ta hannun Hukumarta ta Raya Kasashe Masu Tasowa USIAD, domin ganin an kidaya kuri’ar kowa da kowa a yayiin zaben na 2023 a Najeriya.
A wani labarin na daban Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shaida wa ‘yan kasar su zabi wanda suke so daga kowace jam’iyyar siyasa a yayin zaben shekarar 2023.
Ya ce babu wanda za a bari ya raba kudi ga ‘yan jagaliyar da za su yi barazana ga masu zabe a dukkanin mazabu.
Shugaba Buhari yana bayani ne a birni Landan a ranar Laraba, bayan da ya kammala wata ganawa da sarkin Ingila Charles na 3 a fadar Buckingham.
Buhari ya ce burinsa shi ne ‘yan Najeriya su yarda cewa gwamnatinsa tana ganin girmansu, kuma tana mutunta su, yana mai cewa abin da yake so su tuna kena bayan ya sauka daga karagar mulki.