Wata mata da ake zarginta da aikewa da ambulan mai dauke da wasika mai guba, wacce ta tura ga gidan gwamnatin Amurka, ta shiga hannu.
Jami’an tabbatar da doka sun sanar da mujallar The Associated a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, cewa an kama matar a birnin New York.
An kama wasikar a makon da ya gabata kafin ta isa gidan gwamnatin Amurka. Jami’an hukumar kwastam da bada kariya ga iyakar kasar da ke iyakar gadar Peace suka kamata.
Sun ce dole za ta fuskanci hukunci. Har yanzu basu saki sunanta ba. Wasikar da ta rubuta ga gidan gwamnatin Amurkan an yi ta daga kasar Canada, ‘yan sandan kasar suka tabbatar.
An kama wasikar a wata ma’aikatar gwamnati ne kuma binciken farko ya bayyana cewa an yi ta ga shugaba Donald Trump ne.
Kamar yadda jami’an suka tabbatar amma suka bukaci a boye sunayensu, sun ce binciken farko da aka yi an gano wata guba mai suna ricin ce a ciki.
Ba wannan bane karo na farko da aka fara tunkarar manyan jami’an kasar Amurka da wasika mai dauke da guba ba.
A 2018, an kama wani tsohon sojan ruwa da ya tura wasiku a cikin ambulan ga Trump da wasu makusantansa wanda ke kunshe da muguwar gubar. An kama wasikun kuma babu wanda ya mutu sannan aka damke tsohon sojan.
A 2014, wani mutum daga yankin Mississippi an yanke masa hukuncin shekaru 25 a gidan yari, bayan ya aike wa Shugaba Barack Obama da jami’ansa wasiku masu guba.