Amina Mohammed Ta Yi Tazarce

An sake zaɓen tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya Amina Mohammed a matsayin mataimakiyar sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar Juma’a ne babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya sake zaɓen Antonio Guterres a matsayin Sakatare Janar a wa’adi na biyu na shekara biyar.

Kuma zai ci gaba da aiki tare da Amina Mohammed ƴar Najeriya a matsayin mataimakiyarsa, kamar yadda ta sanar a shafinta na Twitter.

Guterres da Amina za su fara sabon wa’adi a farkon watan Janairun 2022.

Antonio Guterres ya gaji Ban Ki-moon ne a watan Janairun 2017 kafin Donald Trump ya zama shugaban Amurka wanda ya sha caccakar Majalisar Dinkin Duniya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply