Tsohuwar Shugabar Kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi koyi da kasarta Liberia wajen zabar mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, a matsayin Shugabar Kasa mace ta farko a Najeriya ta biyu a nahiyar Afirka.
Misis Sirleaf din ta bayyana hakan ne yayin bukin cika shekara 60 na Amina Mohammed din.
Tsohuwar Shugabar Kasan da take magana a wajen taron da wata cibiya ta kira a Abuja ta bayyana Amina Mohammed a matsayin ‘ikon Allah kuma wacce za ta haifar da maslaha.’
Ta ce Amina Mohammed wacce ta zama ta daban a matan Afirka kuma Shugabar duniya, jigo ce a wajen assasa muradun karni guda 17 da suka mayar da hankali kan batun daidaton jinsi.
A cewar Sirleaf, Amina Mohammed ta cancanta sosai da ta rike mukamin Shugabar Kasa, bisa la’akari da gogewarta a sha’anin shugabanci, da sanin darajar ‘yan Adam.
A baya dai ta taba zama mataimakiya ta musamman ga Ban Ki-moon kan batun tsarin ci gaban duniya bayan shekarar 2015. A 2014, ta kasance guda cikin rukunin kwararru masu taimaka wa kan tattara bayanan dorewar muradun ci gaba daga 2015 zuwa 2016, sannan ta rike mukamin Ministar Muhalli a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Amina Mohammed ta taba rike mukamin babbar mai bada shawara ta musamman ga Shugaban Kasa kan cimma muradun karni na (MDGs hakika ta cancanta da zama shugabar kasa.