Ambaliyar Ruwa: Buhari Ya Ba Minista Wa’adin Daukar Mataki

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba ministan albarkatun ruwa na Suleiman Adamu, kwanaki 90 domin samar da cikakken tsarin da za a bi wajen magance iftila’in ambaliyar ruwa a kasar.

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da aka aike wa ministan, wadda shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari ya sanya wa hannu, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Sanarwar ta ce shugaba Buhari ya umarci ministan da ya yi aiki tare da ma’aikatar kula da muhalli da ma’aikatar sufuri da kuma gwamnatocin jihohi domin tsara matakan da za a bi domin magance matsalar.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar NEMA ta ce kawo yanzu ambaliyar ta shafi kusan mutum miliyan 2.5, yayin da mutum 603 suka mutu a fadin jihohin kasar sama da 20.

Labarai Makamanta

Leave a Reply