Ambaliya: Ɗan Majalisa Ya Bukaci A Biya Diyya Ga Jama’ar Jihar Kebbi

Sakamakon ambaliyar da ya yi sanadiyyar rushewar gidaje, gadaje, gonaki da kadarori na bilyoyin kudi, Dan majalisar tarayya mai wakiltar Koko/Besse da Maiyama dake jihar Kebbi, wato Honarabul Shehu Muhammad Koko (Wamban Koko) ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta waiwayi lamarin domin baiwa al’ummar da lamarin ya shafa tallafi.

Jihar Kebbi dai ta shahara wajen harkar noma amma sai gashi baya ga matsalar corona sai ambaliyar ruwa ta shafi wasu yankunan jihar, wanda hakan ya jawo asarar gadoji, gidaje, gonaki da abubuwan more rayuwa.

Sakamakon haka ne Honarabul Shehu Koko ya kai kudiri gaban majalisar tarayya, inda ya mika koken al’ummar jihar Kebbi tare da neman a duba yiwuwar biyan diyar asarorin da ambaliyar ruwa ta jawo na asarar gonaki, abinci, gidaje, muhalli, gadoji, hanyoyi da sauransu.

Bayan Honarabul Koko ya mika koken, Shugaban majalisar tarayya, Honarabul Femi Gbajabiamila, nan take ya karbi koken. Inda ya bayyana cewa za su yi wani abu kan lamarin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply