Allura Ta Tono Garma: Mailafia Ya Shiga Wasan Ɓuya Da Jami’an Tsaro

Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Dakta Obadiah Mailafia ya garzaya Babban Kotun da ke Jihar Plateau domin neman a kare masa hakkinsa na walwala da adalci bayan da ‘yan sanda suka gayyaci shi zuwa Abuja.

Ana hasashen cewa gayyatar da ‘Yan sanda suka yi wa Mailafia ba za ta rasa nasaba da gayyatar da Hukumar ‘Yan Sandan Farin Kaya, DSS, ta masa ba a kan ikirarin da ya yi na cewa wani gwamnan Arewa na cikin shugabannin Boko Haram.

Da ya ke jawabi yayin taron manema labarai a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, Mailafia ya ce gayyatar da aka yi masa bita da kulli ne, cin mutunci, cin zarafi da yunkurin a bashi tsoro.

Ya bayyana cewa zai shigar da kara a kotu domin kalubalantar gayyatar da rundunar ‘yan sandan ta yi masa.

A rahoton baya bayan nan, an ruwaito cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta aike wa Dakta Mailafia takardar gayyata zuwa Abuja. Ƴan sandan za su fara binciken su ne duk da cewa hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS, tana gudanar da nata binciken a kan zargin da tsohon mataimakin gwamnan CBN ɗin.

Sai dai rundunar ta ƴan sanda ba ta ambaci dalilin gayyatar sa ba a cikin takardar da ta aike masa. Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Umar Sanda ne ya saka hannu a kan wasikar a madadin mataimakin Sufeta Janar na ƴan sanda, sashin masu binciken manyan laifuka, CID, da ke Abuja.

A takardar mai lamba 3000/X/FHQ/ABJ/VOI/245/8, mai ɗauke da kwanan wata 20 ga watan Agusta, ƴan sandan sun bukaci Mailafia ya zo ofishin hukumar sashin masu binciken manyan laifuka, Garki Area 10 Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 da karfe 11 na safe.

Labarai Makamanta

Leave a Reply