Allah Ya Kiyaye Da Jirgin Mu Ya Yi Hatsari – Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta yi maganarta na farko bayan dawowa daga Dubai, hadaddiyar masarautar Daular Larabawa inda ta je jinya.Ta mika godiyarta ga ‘yan Najeriya da suka sanyata cikin addu’o’insu yayinda take kwance babu lafiya a Dubai.

Ta ce yanzu ta warke kuma ta samu lafiya. Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita da daren Asabar, 22 ga Agusta, 2020.

Yayin dawowarta daga Dubai, Aisha ta bayyana cewa jirginsu ya dan samu mishkila cikin hazo amma matuƙan Jirgin sun samu daman shawo kan lamarin.
“Ina son amfani da wannan dama wajen godewa yan Najeriya bisa addu’o’insu yayinda na tafi jinya. Yanzu na warke kuma na dawo gida, Najeriya.” “Yayinda muke hanyar dawowa, jirgin mayakan saman Najeriya ya samu matsala cikin hazo amma babban matuƙin jirgin da abokan aikinsa sun samu nasarar shawo kan lamarin.”
“Ina jinjina da godiya kan matuƙan jirgin bisa namijin kokarin da sukayi.”

A ranar 7 ga Agusta, muka kawo muku rahoton cewa an fita da uwargidan Shugaban birnin Dubai, domin jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas. Yayinda ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

Labarai Makamanta

Leave a Reply