Allah Sa Rasuwar Mahaifin Kwankwaso Ta Zama Silar Daidaita Ganduje Da Kwankwaso – Magaji

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji ya yi addu’ar samun daidaito tsakanin tsohon gwamna Kano,Dr Rabiu Kwankwaso da gwamna Dr Abdullahi Ganduje na jihar Kano.

Tsohon Kwamishinan wanda yanzu shi ne shugaban kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa na aikin janyo bututun iskar gas zuwa jihar Kano ya yi wannan addu’a ce kwana 1 bayan rasuwar mahaifin Sanata Kwankwaso.

Muazu Magaji ya ce yana fatan mutuwar mahaifin Kwankwaso ya zama silar shiryawarsu kamar yadda mutuwar mahaifiyar Ganduje ya zama daga cikin sanadin rabuwarsu, kamar yadda ya bayyana.

“Ya Allah, kamar yadda ka jarrabi bayinka da sabani a lokacin rasuwar mahifiyar Ganduje, Allah ka sa wannan rashi na mahaifin Kwankwaso ya zama silar daidaito a tsakaninsu.”

Da alama maganar tsohon kwamishinan ta birge mutane musamman yadda ake ganinsa mai yawan yin maganganu da suke suke musu kallon sakin layi a kan al’amuran yau da kullin wadda ta kai ana masa lakabi da WIN-WIN Caji wasu kuma suce WIN-WIN Canji.

Labarai Makamanta

Leave a Reply