Ali Ya Ga Ali: Jaafar Jaafar Ya Yi Ido Biyu Da Ganduje A Landan

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya haɗu da mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, a Chatham House da ke birnin Landan a Ingila.

Wannan shi ne karo na farko da Ganduje ya haɗu da Jaafar fuska da fuska tun bayan da mawallafin jaridar ya wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke nuna gwamnan na saka dalolin Amurka a aljihu da ake zargin na rashawa ne.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa su biyun sun haɗu ne a Chatham House, inda dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Nijeriya mazuna Ingila kan manufofinsa idan ya ci zaɓen 2023.

Har yanzu dai jaridar nan ba ta samu bayanin abinda su biyun su ka tattauna ba, sai dai kuma bidiyon ta nuna inda dukkansu su ka yi musabiha cikin dariya da nurmushi kuma su ka rungume juna.

Idan an tuna cewa Jaafar ya koma birnin Landan da zama ne bayan da ya yi zargin cewa ya na fuskantar barazana daga Ganduje sakamakon faya-fayen bidiyo ɗin da ya wallafa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply