Albashin ‘Yan Majalisa Bai Taka Kara Ya Karya Ba – Ndume

Sanata mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya soki kiran da ake yi na rage albashin ‘yan majalisar dokokin tarayya inda ya ce shi a ganinsa albashin ‘yan majalisar bai da wani tasiri kan tattalin arzikin kasar.

Ndume, ya bayyana hakan ne a yayin da aka yi masa wata tambaya a cikin wani shirin Channels Television na yammacin ranar Juma’ a, 25 ga watan Oktoban 2020.

Dan majalisar mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin cewa ‘yan majalisar sun samu naira biliyan 128 ne kacal a kasafin shekarar 2021 na sama da naira tiriliyan 13.

A cewarsa, hakan na nufin idan aka cire abin da aka kasaftawa majalisar, za a samu ragin naira biliyan 128 kenan, toh amma shin akwai wani banbanci da hakan zai kawo a kasafin kudin.

Ya ce mutane irin sa sun zo majalisa ne domin yi wa al’umma aiki ba wai don su azurta kawunansu ba.

Ndume ya yi korafin cewa babu wani dan majalisa da ya taba tara kudi saboda ya kasance a majalisar tarayya.

“Babu wani dan majalisa, ku je ku duba tarihi, babu wanda ya zama mai kudi saboda ya taba rike mukamin dan majalisa,” in ji Ndume.

A cewarsa, tun da ya shiga siyasa a 2003, rayuwar sa bata sauya ba, sai dai ya ce lallai matsalar kasar nan ita ce tsadar shugabanci a dukkanin matakan gwamnati.

Sanatan ya bayyana cewa ba zai yiwu a rika alakanta tsadar gwamnatin da majalisar dokokin tarayya ita kadai ba.

Ya bayyana cewa baya ga albashi, kasafin da aka ware wa ‘yan majalisar tarayya a ciki ne za a aiwatar da komai da biyan ma’aikata.

Ku kasance da shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun labarai da dumi dumin su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply