Alaramma Ya Fasa Ƙwai, Ya Fallasa Yadda Aka Saye Malamai A Zaben 2023

IMG 20240512 WA0041

Alaramma Ismail Maiduguri ya zargi wasu daga cikin malaman musulunci da kiristanci da biyewa ‘yan siyasa lokacin zabe

Malamin Al-Kur’anin ya ce yawan cikan sahu a masallatai da coci ake amfani da su a wajen sayen bakin malamai

Gwani Ismail Maiduguri ya ce tun da an karbi kudin ‘yan siyasa, dole yanzu ba za a iya kokawa da irin mulkinsu ba

Ismail Maiduguri ya tofa albarkacin bakinsa game da halin da Najeriya take ciki a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.

Alhafiz Ismail Maiduguri ya ce a yanzu ‘yan siyasa sun fahimci cewa za a iya yin amfani da abin duniya a saye kuri’u lokacin zabe.

Wani bidiyon malamin a shafin X ya nuna shi yana bayanin yadda aka yi amfani da taliya wajen samun goyon bayan talaka a bara.

Baya ga talakawa, ya ce masu mulkin yau sun yi amfani da dukiyarsu wajen rufa bakin wasu malaman addinin musulunci da kirista. Akwai malamai na Allah a Najeriya Wannan malami ya ce ba a taru an zama daya ba, amma akwai jagororin addini da suka cefanar da matsayin da Ubangiji ya ba su. “Akwai malamanku da fastoci da ke cewa a zabi wane da kyakkyawar niyya. Amma akwai da yawa da ciniki ake yi da su.” “Iyakar yawan masu yi masa (malami) kabbara ko halleluiah a coci, iya yawan kudin da za a ba shi (Fasto, Fada ko Rabaren).”

Ismail Maiduguri ya yi ikirarin bayan zabe ba a jin wani ya fito ya ce uffan saboda kudi ne suka yi aiki wajen samun shugabanci.

Malamin yake cewa ko da farashin man fetur ya tashi, sai dai a ji masana addini suna fadawa talaka ya kara hakuri kuma ya tuba.

Bayanan sun zo ne a wajen karatun littafin da ya fara game da tarihin mata da mazan da ka kewaye da Annabi Muhammad SAW. Sa’ad Yusuf Abu Azeez ya rubuta fitaccen litafin da malamin yake karantarwa a masallacin Zone B a rukunin gidajen ‘yan majalisu.

Sai dai Ismail Maiduguri yana ganin akwai laifin talaka domin ba tursasa masa aka yi, shi da kan shi ya zabi wadanda aka tallata masa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply