Likitoci sun bayyana cewa mai ciki za ta ga wasu alamomi da ke nuna mata cewa ta yi bari.
Wasu daga cikinsu sun hada da ciwon mara da zuban jini ko fitan gudan halittar mutum ko zuban ruwan da dan tayi ke kwanciya a ciki.
Sannan duk wasu alamu da mai ciki ke ji da suka hada da tashin zuciya da kasala duk za ta daina jinsu.
Bincike ya nuna cewa bari babbar matsala ce a Najeriya, inda kashi 30 cikin dari na masu juna biyu ke yin bari.
A likitance cikin da ya zube kasa da wasu ‘yan makonni da samunsa, shi ake kira bari.
Kuma hakan ya bambanta a tsakanin mata a sassa daban-daban na duniya.
Likitoci sun bayyana cewa a kasashe masu tasowa da suka hada da wasu kasashen Afrika, macen da cikinta ya zube kafin makonni 28 shi ake kira bari.
Yayin da a nahiyar Turai kuma a kan ce mace ta samu bari ne idan cikinta da ya zube kafin mako 24 ba.
Cikin da ya zube kafin mako 22, shi ake dauka an yi barinsa a Amurka.
Masana a fannin kiyon lafiya na bayar da shawarar cewa, duk macen da ta ga wani alamu na bari ta garzaya asibiti.
Hakan a cewarsu yana da muhimmanci saboda kaucewa matsalolin kiwon lafiyar da ka iya biyo baya.
Manya daga cikin wadannan matsaloli su ne na zuban jini mai yawa, wanda hakan ka iya shafar zuciya da koda.
Haka kuma kwayoyin cuta za su iya shiga jikinta, ko mahaifarta ta fashe idan wanda ba kwararre ba ya yi mata wankin ciki.
Sannan akwai yiwuwar idan mace ta yi bari ta sake yin wani.