Duk da cewa hukumar DSS ta musanta rahoton cewa ta damke mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.
Da misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ta kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami’an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa.
Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu
- Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati
- Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn
- Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya
- Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya
- Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu
- Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn
- Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace
- Fifita wasu jami’an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da ‘Magu Boys’
- Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba
- Sayar da dukiyoyin sata ga yan’wansa, abokan arziki da abokan aiki.
A ranar Litinin, an gayyace Ibrahim Magu, fadar shugaban kasa domin amsa tambayoyi da wasu tuhume-tuhume da ake yi masa kimanin 22.
Lauyan Magu, Oluwatoyin Ojaomo, ya ce kwamitin bincike ya gayyaci Magu ne domin ya yi bayani a kan gibin da aka samu a adadin kudin da EFCC ta saka a aljihun gwamnati da kuma wanda Magu ya sanar a bainar jama’a.
A cewar Lauyan, adadin kudin da Magu ya mayar aljihu gwamnati sun zarce adadin kudin da ya sanar EFCC ta kwace. Lauyan ya ce masu son ganin maigidansa sun fi annobar korona karfi.
Idan kana yaki da cin hanci, ka sani cewa cin hanci zai yakeka, cin hanci ya yi karfi sosai, ma su cin hanci sun yi karfi, sun fi annobar korona karfi.” A cewarsa.