Al-Mundahana: Kotu Ta Hana EFCC Kama Tsohuwar Ministar Mai

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta hana takardar amincewa hukumar EFCC izinin cafke Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur.

Alƙali Ijeoma Ojukwu, mai shari’ar, ta ki amincewa da bukatar EFCC ne saboda gazawar hukumar na gabatarwa kotun shaidar kotu na kiranye ga ministar a baya.

Ta ce ya zama wajibi a gabatarwa kotu takardar shaidar goron gayyatar kotu ga tsohuwar ministar, kafin kotun ta amince ta bayar da izinin cafke Alison-Madueke.

Mai shari’ar ta ce, bayar da takardar goron gayyata ga mutum, ba takardar banza bace, dole EFCC ta gabatar da makamanciyar takardar da kotun ta aikawa Alison.

Hukumar EFCC ta shaidawa kotun cewa ofishin Antoni Janar na kasa da ma’aikatar shari’a na bukatar izinin cafke tsohuwar ministar ne, don samun damar dawowa da ita kasar.

“Tuni na bi diddigin bukatar mai shigar da karar. Umurnin kotu na farko da ta bayar ya ci karo ne da sashe na 831 na dokar ACJA,” a cewar mai shari’ar.
“Ya zama nawa nazarin cewa takardun goron gayyatar da muka aikawa wacce ake tuhumar zai taimaka wajen zama hujja ga ofishin AGF. “A yau, wacce ake tuhumar ba ta cikin kotu kuma ba a bayar da dalili ba.

An sanar da ni cewa, ana da yakinin cewa, wacce ake tuhumar yanzu haka tana kasar Burtaniya. “Haka zalika, muna da rahoton cewa yunkurin hukuncin kan mai laifin ya ci tura sakamakon rashin kasancewar izinin cafke wacce ake zargi.

“Amma idan haka ne, ya kamata bangaren da ke kara su mika bukatar neman izinin tare da hujjoji daga ofishin Antoni na kasa.
“Da wannan, na ke ba ku lokaci domin ganin cewa kun aikata komai akan doka da oda.”

An dage sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Disamba 2020, domin tattara hujjoji tare da gurfanar da wacce ake karar gaban kotu.

Labarai Makamanta