Al-Mundahana: Babu Gaskiya A Zargin Da Ake Yi Mini – Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulazeez Abubakar Yari, ya karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suka yada cewar kotu ta umarci a kwace kudin hannun sa dala milliyan 621.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan Abdulrahaman Yahaya, ya bayyana haka a yayin da yake Alla-wadai akan labarin a cikin wata takarda daya rabawa manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

” Abdulrahaman, ya ce gaskiyar labarin shi ne kotu ta umarci a rufe asusun ajiya na tsohon gwamnan a bankunan Polaris da Zenith mai dauke da kudi naira milliyan 278.

” Ya ce labarin farko na Dala Amurka milliyan 621 da aka yada ba gaskiya ba ne, amma gaskiyan kudin shi ne naira milliyan 278.

Abdulrahaman, ya bukaci kafafen yada labarai da su rika tantance labari kafin su yada shi ga alumma domin gujewa duk wani abu da zai kawo rudani.

Sannan kuma ya bukaci ‘yan jarida su guji bari ‘yan-sisaya na amfani da su wajen batawa wani suna saboda biyan bukatun su.

Ya kara da cewa wasu masu bukatar neman wata kujerar sisyasa ne ke kokarain batawa tsohon gwaman Abduazeez Abubakar Yari suna, domin cimma manufarsu kuma ba zasu yi nasara.

Ya ce akwai bukatar al’ummar Najeriya su sani cewar lokacin siysasr bata suna ta wuce ,yanzun lokaci ne na siyasar ci gaban al’umma, sannan kuma mai mutum ya yi ko kuma zai yi kafin azabe shi, saboda mutanen najeriya sun waye sosai akan siyasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply