Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aikawa majalisar dattijai sunayen mutane 8 domin amincewa da su a matsayin sabbin alkalan kotun koli.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aika yayin zaman majalisa na ranar Talata.
Hukumar kula da bangaren shari’a (NJC) ta amince da sunayen manyan alkalan da shugaba Buhari aikawa majalisar dattijai, a cewar Sanata Lawan.
Sunayen mutanen da Buhari ya aika sun hada da;
1- Lawal Garba: Shiyyar Arewa Maso Yamma
2- Helen Ogunwumiju: Shiyyar Kudu Maso Yamma
3- Abdu Aboki: Shiyyar Arewa Maso Yamma
4- M M Saulawa: Arewa Maso Yamma
5- Adamu Jauro: Arewa Maso Gabas
6-Sauel Oseji: Kudu Maso Kudu
7- Tijjani Abubakar: Arewa Maso Gabas
8- Emmanuel Agim: Kudu Maso Kudu
Kazalika, shugaba Buhari ya aikawa majalisar dattijai sunayen mutane biyu da ya ke burin nadawa a matsayin jakadun Najeriya a kasashen waje. Mutanen sune;
Muhammad Manta daga jihar Neja da Yusufu Yunusa daga jihar Yobe.
A cewar Buhari, mutanen biyu za su maye gurbin Air Commdore Peter Gana (mai ritaya) da Alhaji Yusuf Muhammad wadanda a baya aka aika sunayensu zuwa majalisar dattijai domin tantancewa.