Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed, ya ce wasu kungiyoyin waje suna kawo cikas wajen yaki da ake yi da ta’addanci a Najeriya, wanda hakan ke taimakawa wajen sake mayar da hannun agogo baya a ?o?arin da Shugaban ?asa Buhari ke faman yi na samar da tsaro.
Minista Lai Mohammed ya yi wannan magana a ranar Litinin, 4 ga watan Junairu, 2020, inda ya kama sunan Amnesty da ICC. Ministan ya ce kungiyar Amnesty International mai kare hakkin Bil Adama da babban kotun Duniya sun jawo mana matsala a yakin Boko Haram.
Lai Mohammed ya ce barazanar takunkumin da wadannan kungiyoyi da kotun Duniya su ke yi wa Najeriya, ya na karya kwarin gwiwar dakarun sojoji, da mayar da al’amurra baya.
A cewar Ministan, abin da wadannan manya su ke yi bai da wani amfani face taimakawa ‘yan ta’addan, wanda hakan ya jefa Najeriya a matsala.
“Najeriya ba ta shiga ICC domin a rika wasan dan-waken zagaye da ita ba.” Inji Alhaji Mohammed. “Da takaici a ga kungiyar kasar waje ta na kawowa kasar da ta ke fada da ‘yan ta’adda da tsageru matsala bayan ta shiga kungiyar don ganin damanta.”
Duk da wannan gungu da aka yi wa Najeriya, kasar ta samu nasara sosai wajen yakar ta’addanci da tsagerun da su ka addabe ta kuma ta yi rawar ganin da kowa ya shaida inji shi.