Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar tsaro ta Kasa ta yi karin haske kan matsayin Gwamnatin Tarayya dangane da shari’ar shugaban haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.
Majalisar ta ce har yanzu Kanu na da sauran tuhume-tuhume a kanshi sannan da akwai shari’ar da zai amsa.
Kotun daukaka kara a Abuja a ranar Alhamis, ta soke tuhumar ta’addanci da ake yi wa Kanu, abin da ya janyo cece-kuce a bangarori da yawa na kasar.
Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya ce ba a wanke Kanu ba saboda akwai wasu tuhume-tuhumen da ake masa har yanzu kuma ya zama dole ya fuskance su.
Ita ma Majalisar Tsaro ta kasa, wacce Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wa jagoranci, ta ce gwamnati na duba mataki na gaba da za ta dauka akan hukuncin da kotun ta yanke na wanke Nnamdi Kanu.
Da ya ke yi manema labarai jawabi bayan taron majalisar, Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, tare da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, sun ce za a cimma matsaya kan abin da zai faru da Kanu cikin yan kwanaki masu zuwa.
“Kazalika, an yi magana kan Kanu kuma an yi wa majalisar jawabi kan inda aka tsaya kuma an lura an sallami Kanu amma ba a wanke shi daga tuhume-tuhume ba. “Don haka, gwamnati na duba matakin da ya dace ta dauka kan batun kuma za ta sanar da yan Najeriya matsayar ta kan lamarin a nan gaba.”