Tsohon shugaban ?asa na mulkin Soja, Janar Abdulsalami Alhaji Abubakar mai ritaya, ya yi tsokaci gami da garga?in ‘yan Najeriya kan yawaitar Miliyoyin muggan makamai dake karakaina a fa?in kasar nan.
Janar Abdulsalami Abubakar ya ce da akwai muggan makamai dake shawagi a cikin Najeriya sama da miliyan Shida ba bisa ?a’ida ba, kuma sun wadatu a hannun ‘yan ta’adda.
Abdussalami Abubakar, wanda shine shugaban kwamitin zaman lafiya a Najeriya (NPC) ya yi wannan garga?i ne a wani taro da suka yi da masu ruwa da tsaki a Abuja ranar Laraba.
Abdussalami ya ce, yawaitar makaman a ?asa shine yake jawo ?aruwar matsalolin tsaro da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 80,000 galibin su mutanen Arewa.
Ya ce ?alubalen da ?asar nan ke fuskanta bawai rashin tsaro ne ka?ai ba, akwai wasu matsalolin na rayuwa masu nasaba da talauci da kuma jahilci dake cigaba da mayar da hannun agogo baya.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana ?alubalen da Najeriya ke fuskanta kamar; Rikicin Boko Haram, fashi da makami, satar mutane domin neman ku?in fansa, ?aruwar talauci da tsadar rayuwa, kira ga rarraba ?asa da wasu ke yi, ta ko’ina abin babu sauki.
Ya ?ara da cewa akwai ?alubalen yunwa da rashin tsaro ke jawo wa, wanda manoma ke fuskanta kuma suke cigaba da fuskanta, da dai sauran su. Ya ce wata matsalar kuma itace yawaitar muggan makamai dake yawo, ba wai a wasu yankuna ka?ai ba, a fa?in ?asar baki ?aya.
Ya kara da cewa a halin yanzun ana ?iyasin akwai sama da makamai miliyan Shida dake yawo a fa?in ?asar nan. Wanda wannan shine yake ?ara yawaitar matsalolin tsaro, wanda ya jawo mutuwar mutane sama da 80,000 da kuma fitar da mutane kusan miliyan uku daga mahallinsu.
Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce jami’an tsaron mu zasu yi matu?ar ?o?ari wajen shawo kan matsalar idan aka samar musu da makaman da yakamata da ku?a?e yadda yakamata.