Akwai Matsalar Tsaro A Yankin Gamawa – Gwamnatin Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi tace akwai Barazanar matsalar tsaro a yankin Katagum a sanadiyyar shiga Gaidam da Yan Boko Haram sukayi ta Jihar Yobe a kwanan baya, wacce suke makubtaka da kananan hukumomin hudu na Jihar Bauchi, babu bullar Boko Haram kamar yadda wasu rahotanni suka dauka a baya

Hakan ya fito ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabiu Baba, bayan wani zama na gaggawa da gwamnatin tayi da shuwagabanin Jami’an tsaro na dukkan fadin jihar.

Sakataren ya kara da cewa rahotanni na nuni da cewa kana nan hukumomin da abun ya shafa, sun hada da Gamawa, Zaki, Dambam da Darazo cikin Jihar yace Kuma Jami’an tsaro sun kama mutum hudu wadanda ake zargin suna da hannu wajen barnata kayan sadarwa mallakar MTN a Karamar hukumar Gamawa.

Hakan nan Sabiu Baba yace a dalilin haka yasa Jami’an tsaro ala’tilas za a tura masu, Karin karfi tare da Jami’an tsaro na yan’banga da sauransu a yankin musamman kan iyakar Jihar Yobe da Bauchi.

Shima kwamishinan Yan’Sanda na Jihar Sylvester Abiyodun Alabi yace Jami’an su sun kasance cikin Shirin ko ta kwana tun samun labarin abunnda ya ya faru a Gaidam, yace zasu tsaurara matakan tsaro da zagaya wa lungu lungu, ba tare da wani bata lokaci ba,

Kana yace a cikin mutanen da ake Zargin bata kayan sadarwan kuwa yace Jami’an tsaro sun chafke sune saboda alaka da suke dashi na aukuwar hakan a yankin na karamar hukumar Gamawa.

Biyodun Alabi, ya kara kiran mutane a yankin da su kwantar da hankalinsu Kuma susa Idanu sosai duk inda suka ji wani abu to suyi saurin sanar da Jami’an tsaro dake kusa da su, don a dakile su, a cewarsu sai kowa ya bada tasa gudummuwar sannan za aci nasarar yakan Yan ta’adda a ko ina.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment