Akwai Lauje Cikin Na?i A Hare-Haren Da Ake Kaiwa ‘Yan Arewa – Dr. Hakeem

An tabbatar da cewar da akwai lauje cikin na?i dangane da rikice-rikicen kabilanci dake faruwa a yankin Kudancin Najeriya, musanman a Shiyyar Kudu maso yammacin ?asar tsakanin ‘yan Arewa da al’ummar Yarbawa lamarin da ya ?azamta har ya kai ga asarar rayuka da dama.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin sanannen dattijon nan mazaunin garin Kaduna Dr. Hakeem Baba Ahmad a yayin tattaunawar shi da wakilinmu dangane da halin da ?asa ta tsinci kanta a ciki na ?arkewar rikicin kabilanci a sashin Kudancin Najeriya.

Baba Ahmed wanda jigo ne a cikin ?ungiyar Dattawan Arewa, ya bayyana cewar a magana ta gaskiya an samu sakaci da gazawa a bangaren gwamnati wajen da?ile wannan matsala, lamarin da ya taimaka wajen ?ara dagulewar lamurra.

“An wayi gari a yau an samu wani mutum da ya ke bugun kirji wajen kisan jama’a a kudu, kuma har ya zama wani tauraro a cikin jama’arsa amma shiru a bangaren gwamnati ba a ?auki wani mataki na kamawa gami da hukunta shi ba, wanda hakan gazawa ce babba a Gwamnati”.

Hakeem Baba Ahmed ya kuma yi kira da babbar murya ga ‘yan Arewa musamman Matasa da su kula sosai kada a samu wasu suyi wani yunkuri na cewar za su ?auki fansar abin da ke faruwa anan Arewa, domin hakan babu abin da zai haifar illa sake dagulewar al’amurra.

Dattijon Arewan ya ce dukkanin wadannan rikice rikice na faruwa ne bisa ga dalilai na siyasa, a kokarin da ‘yan kudu suke da shi na ganin mulki ya koma kudanci ko ta halin ?a?a a shekarar 2023.

Dr. Hakeem Baba Ahmed ya kuma bayyana goyon bayan ?ungiyar su akan dukkanin abin da za’a yi wanda zai kawo maslaha da fahimtar juna tsakanin ‘yan Najeriya.
“Muna goyon bayan gudanar da babban taro na ?asa muddin hakan zai haifar da samun mafita a halin tsaka mai wuya da kasar ke ciki”.

Related posts

Leave a Comment