Akwai Lauje Cikin Naɗi A Ganawar Kungiyoyin Arewa Da ‘Yan Takara

‘Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan zaman su da kwamitin shugabannin Arewa. Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi wasu daga cikin ‘yan kwamitin da niyyar tsaida wani ‘dan takara.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan na NNPP, Hon. Jibrin ne ya fitar da jawabi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba 2022.

“Muna da bayanai masu karfi a wajenmu da ke nuna cewa wasu mutane sun kammala shirin maida tsarin wata damar tallata wani ‘dan takara. Mun yi imani cewa ba daidai ba ne wasu mutane ko wata kungiya ta goyi bayan wani ‘dan takara ta bayan-fage da sunan yankin Arewacin Najeriya.

Musamman a lokacin da muke da ‘yan takara fiye da daya daga yankin na Arewacin Najeriya. Saboda haka muna ba ku shawarar ku gujewa wani abin da zai bata sunan Ahmadu Bello da sauran manyan Arewa irinsu Tafawa Balewa, Aminu Kano, Sir Kashim Ibrahim da J.S. Takra, ta hanyar goyon bayan ‘dan takaran da bai shahara ba, a maimakon wanda ya fi shahara, ya fi sanin aiki, ya fi nagarta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply