Akwai Lauje Cikin Naɗi A Ɗaukar Ma’aikata 774,000 – Majalisa

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, ya ce bai wa ‘yan majalisar gurabe talatin- talatin na daga cikin gurabe 1,000 a duk karamar hukuma bai dace ba kuma babu adalci.

Shugaban marasa rinjaye kuma dan majalisa daga jihar Delta karkashin jam’iyyar PDP, Ndudi Elumelu ,ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a kan ayyukan.

Ya ce a matsayin wakilai na jama’a, bai kamata a ba su gurabe 30 ba a mazabunsu.

Elumelu ya ce suna bukatar adalci a wurin sharuddan bada guraben aikin.

Ya zargi sharuddan da bai wa ‘yan jam’iyyar APC fifiko kuma hakan illa ne ga ‘yan Najeriya.

Ya tabbatar da cewa guraben ayyukan 774,000 da aka bada na talakawa ne kuma ta wannan hanyar ne kadai za a iya tallafawa talakawan.

Kamar yadda yace: “Guraben mutum 30 ga dan majalisa a kowacce karamar hukuma bai dace ba kuma ‘yan Najeriya ba za su yarda da hakan ba.

“A matsayinmu na wakilan jama’a, mun fi kusanci da su kuma muna tattaunawa da su kai tsaye ba tare da banbancin siyasa ko addinai ba.

“Dukkan ‘yan Najeriya da ke mazabunmu suna da hakki a kanmu ba tare da duban banbancin siyasa ba. A don haka dole ne a sake duba lamarin.

“Hakazalika, wadanne sharudda ne aka duba har aka ba mu gurabe talatin- talatin?

“Ta yaya za mu tabbatar da cewa shirin ya amfani ‘yan Najeriya?”

Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta duba shirin don tabbatar da cewa talakawa sun amfana.

Labarai Makamanta

Leave a Reply