Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ?asa (NHIS), Farfea Yusuf Usman, a ranar Laraba ya ce ?an bindiga da suka addabi yankin Arewa na da layukan kiran wayar gwamnonin yankin, kamar yadda Jaridar Vanguard ta rawaito.
Ya bayyana ?an siyasa a matsayin wa?anda suka fi ?an bindiga hatsari da ?arna sakamakon satar ku?a?en ?asa su siyawa matasa bindigu don magu?in za?e, sannan daga baya su yi watsi da su.
Malam Yusuf, wanda ya bayyana hakan a gidan jaridar ARISE, ya ce a wasu lokutan, gwamnonin jihohin suna siyawa ?an bindigar Shanu, sannan su ba su ku?i a matsayin hanyar tausar su.
“Da yawa daga cikin ?an bindigar suna da layukan gwamnonin, suna kiransu. Na san Nasir El-Rufa’i ya ?i yin sulhu da su.
Gwamnoni na yin sulhu da su, su na siya musu shanu, suna siya musu kaji da tsuntsaye, dukkan wannan na nuni da gazawar gwamnati daga jihohin.
Ya ?ara da cewa “Kasan ire iren ?an fashi kala biyu ne akwai ?an fashin daji masu ?auke da bindigu da kuma ?an fashi masu yawa a gwamnati.”
Duk mutanen nan masu sace ku?a?en gwamnati sun fi ?an bindiga hatsari. Dukkan ?an siyasa masu satar ku?i sun fi ?an bindiga hatsari, kuma su na cin za?e.”
Malam Yusuf yace rashin tsaron ?asar nan ya samo asali ne saboda rashawa da azzalumar gwamnati.
‘?an siyasa sune masu shigo da muggan ?wayoyi irinsu Tramol, su bawa matasa, su maida su ?an daban siyasa. Suna basu makamai kuma da zarar an ci moriyar ganga, sai a yada korenta.
A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.