Akwai Kyakkyawar Alaka Tsakanin ‘Yan Bindiga Da Gwamnonin Arewa – Farfesa Usman

Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfea Yusuf Usman, a ranar Laraba ya ce ƴan bindiga da suka addabi yankin Arewa na da layukan kiran wayar gwamnonin yankin, kamar yadda Jaridar Vanguard ta rawaito.

Ya bayyana ƴan siyasa a matsayin waɗanda suka fi ƴan bindiga hatsari da ɓarna sakamakon satar kuɗaɗen ƙasa su siyawa matasa bindigu don maguɗin zaɓe, sannan daga baya su yi watsi da su.

Malam Yusuf, wanda ya bayyana hakan a gidan jaridar ARISE, ya ce a wasu lokutan, gwamnonin jihohin suna siyawa ƴan bindigar Shanu, sannan su ba su kuɗi a matsayin hanyar tausar su.

“Da yawa daga cikin ƴan bindigar suna da layukan gwamnonin, suna kiransu. Na san Nasir El-Rufa’i ya ƙi yin sulhu da su.

Gwamnoni na yin sulhu da su, su na siya musu shanu, suna siya musu kaji da tsuntsaye, dukkan wannan na nuni da gazawar gwamnati daga jihohin.

Ya ƙara da cewa “Kasan ire iren ƴan fashi kala biyu ne akwai ƴan fashin daji masu ɗauke da bindigu da kuma ƴan fashi masu yawa a gwamnati.”

Duk mutanen nan masu sace kuɗaɗen gwamnati sun fi ƴan bindiga hatsari. Dukkan ƴan siyasa masu satar kuɗi sun fi ƴan bindiga hatsari, kuma su na cin zaɓe.”

Malam Yusuf yace rashin tsaron ƙasar nan ya samo asali ne saboda rashawa da azzalumar gwamnati.

‘Ƴan siyasa sune masu shigo da muggan ƙwayoyi irinsu Tramol, su bawa matasa, su maida su ƴan daban siyasa. Suna basu makamai kuma da zarar an ci moriyar ganga, sai a yada korenta.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply