Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina ganin fitinar da ke faruwa a jihohin arewa maso gabashin jihohin Borno, Yobe da Adamawa a matsayin matsalar arewa; kalubale ne da ya shafi kowa da kowa.
Zulum ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani na shekara ta 17 na Gani Fawehinmi wanda Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, reshen Ikeja ta shirya ranar Juma’a. A cewarsa, mambobin kungiyar ta Boko Haram sun hada da fararen fata, ‘yan Asiya, ‘yan Afirka, Musulmai da Kirista.
Gwamnan ya danganta fitina da ta’addancin da ake yi a kasar ga yawaitan rashin aikin yi, talauci, da kuma shan muggan kwayoyi, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su guji nuna son kai, kabilanci da kuma ra’ayin amfani da addini wajen haifar da rarrabuwa.
Ya kara da cewa ya maye gurbin tsohon Shugaban Ma’aikatansa, wanda dan uwansa Musulmi ne, da Kirista, saboda ya fifita cancanta sama da biyayya. Ya ce wannan ne karo na farko da Kirista zai hau kujerar a jihar. “Ni dan jihar Barno ne, kuma yawancin ‘ya’yanmu suna cikin Boko Haram. Ba na musun fadin gaskiya. Amma kuma, mutane da yawa suna ɗaukar nauyin su a faɗin duniya. Daga cikin Boko Haram, muna da fararen fata, ‘yan Asiya, ‘yan Afirka, Musulmi da Kirista,” in ji Zulum.
“Dole ne mu daina ganin wannan fitinar a matsayin matsalar Arewa. “Tazarar da ke tsakanin jihar ta Borno da ta jihar Legas ta kai kimanin kilomita 1,700, amma fa ku kula idan jihar ta Borno ba ta da zaman lafiya, sauran bangarorin kasar nan ba za su taba zama cikin lumana ba.
Mun ga abin da ya faru a Libya, Iraki da sauran ƙasashe. Gina zaman lafiya da haɗin kan jama’a suna da matukar mahimmanci wajen ƙarfafa ƙarfin al’ummominmu.
“Har sai mun kawar da son zuciya, kabilanci da kuma amfani da addini, kafin mu samu daidai a kasar nan. “Tsarin mulki ya bayyana karara kan bukatar zaman lafiya a tsakaninmu baki daya, shi yasa ma aka sanya tsarin dabi’ar tarayya a cikin kundin tsarin mulki, amma an ci zarafinsa.”