Akwai Hannun ‘Yan Siyasa A Taɓarɓarewar Tsaro: Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce akwai hannun ‘yan siyasa a kalubalen tsaron da su ka dabaibaye kasar nan.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi a wani sansanin sojoji na musamman da ke garin Faskari.

“Mu ‘yan siyasa, ya kamata a zarga a kan batun kalubalen rashin tsaro da ya ki karewa a tsakanin jama’armu.

A bayyana take cewa wasu ‘yan siyasa su na amfani da kalubalen tsaro a kasa domin biyan bukatar kansu.

Irin wadannan ‘yan siyasa ba za su taba yabon rundunar soji ba saboda ta samu nasara a fagen yaki da ‘yan ta’adda.

Amma, nan da nan, za ka ji muryarsu a kafafen yada labarai domin sanar da harin ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda.

Irin wadannan ‘yan siyasa ba su damu da kishin kasa ko jama’a ba, burinsu kawai shine su makale a kan mulki ta kowanne hali,” a cewar Matawalle.

Kazalika, ya bayyana cewa ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kadai keda alhakin tabbatar da tsaro ba a kasa.

Ya kara da cewa gwamnonin, shugabannin hukumomin tsaro da sauran ‘yan kasa ma su kishi su tashi tsaye wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a tsakanin jama’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply