Shahararren Malamin addinin musulunci a jihar Kano, Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya ce duk abunda ke faruwa na zubar da jini da kashe rayukan mutane a kasarnan da hannun wasu manyan kasarnan yan Arewa musulmi a ciki kuma shugaban kasa ma ya sani, munafurci yasa ake boyewa ba a son a fada.
A wani bidiyo mai tsawon minti 01:03 da wakilin mu ya kalla ya ji Shehin Malamin yana cewa ” Duk abunda kuka ga anayi a kasar nan na zubar da jini da kashe mutane wallahi akwai hannun yan Arewa musulmi manyan kasar nan a ciki, kurum munafurci ne akeyi ba a fada. Yanzu da ka zo ka tara [mutane ka fada] …kayi kaza sai kaga an turo security (jami’an tsaro) a kira ka [ana yi maka mazurai] meye za ayi kaza shikenan basa so a fada.”
“Amma a matsayin ku na yan kasa wallahi wajibi ko zasu kashe mu gwanda mu gaya muku wannan shine hakikanin abinda yake faruwa kurum”
Dr. Gadon kaya ya cigaba da cewa “Kuma shi shugaban kasa da kuke gani ya san da wannan abun amma wallahi yafi karfinsa sai dai da taimakon wasu..”
“Yanzu in ya turo sojoji ko ya tura yan sanda ko wani abu to ai akwai masu basu umurni. Suma manyan sojojin ba suna da interest (buri) na samun kudi ba… suna dashi! To haraka ce ta tsiya, me zan samu kurum. Dan Nigeria ya yarda ayi ta kashe dan’uwansa indai zai samu arziki”
“To wallahi Malam akwai son zuciya ne kar kuyi mamaki kuga wai abunnan yaki ci yaki cinyewa wallahi akwai son zuciya ne.” Inji Shehin Malamin