Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar agajin gaggawa a Najeriya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun hadarin jiragen sama a kasar, sakamakon yawan ruwan saman da za a gani a daminar bana da kuma yanayin da filayen jiragen saman kasar su ke.
Shugaban hukumar Mustapha Habib Ahmed ya yi wannan gargadi lokacin da ya ke gabatar da rahoto kan kalubalen da ake fuskanta a kasar cikin wannan shekara ta 2021 da suka shafi daminar bana.
Tsagewar hanyoyin saukar jiragen sama da tsawa da kuma ambaliya na daga cikin abinda hukumar ta ce ke iya haifar da matsalar sauka da tashin jiragen sama wanda zai iya shafar na’urar da ke taimakawa jiragen sauka da tashi da kuma haifar da hadari.
Ahmed ya ce ambaliyar da za a samu a tashoshin jiragen saman sakamakon yawan ruwan da ake saran samu bana na iya haifar da matsaloli ga matafiya cikin motoci saboda barazanar lalata gadoji da kuma wanke hanyar motar.
Shugaban ya ce rahoton hukumar da ke kula da yanayi ta kasa kan yawan ruwan saman da za a gani bana wanda ba a saba ba na iya haifar da ambaliya a jihohin Borno da Yobe da Bauchi da Oyo da Enugu da Anambra da kuma Akwa Ibom.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumomin Najeriya ke gargadin jama’ar kasar saboda barazanar da ake fuskanta bana sakamakon yawan ruwan saman da za a gani.