Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana muradunsa ga al’ummar jihar Benue. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, wanda ya bayyana hakan ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba a taron cocin 82nd Synod of the Universal Reformed Christian Church, aka NKST, a Mkar, jihar Benue ya ce zai cigaba da kasancewa tare da al’ummar Benue kamar yadda yayi a baya.
Atiku wanda ya samu wakilcin Farfesa Iorwuese Hagher da Hanarabul Chille Igbawua na kwamitin kamfen PDP, yace: “Jam’iyyata PDP mai hankali ce ga rabon mulki tsakanin Kiristoci da Musulmai a kasar nan.”
“Wadanda suka ki girmama addininmu sun yi hakan ne da gayya. Ba zamu bari su tsira ba.” Atiku Yace al’ummar Benue su zabesa Atiku ya yi kira da jama’ar Benue su daina yi masa kallon Bafillatani amma a matsayinsa na Atiku Abubakar.