Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, yace akwai wani abu da ya ha?asu inuwa ?aya da gwamnonin tawagar G5 karkashin jagorancin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Tawagar G5 ta ?unshi Wike, Samuel Ortom na jihar Benuwai, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ipeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, dukkansu basu ga maciji da ?an takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
“Gwamnonin G5 kamar yadda suka ra?a wa kansu sun kira kansu da ‘Tawagar gaskiya’. Kamata ya yi ace ina tare da su amma basu neme ni ba saboda wani dalili da su ka?ai suka sani.” “Amma ina da ala?a mai ?arfi da su, kowane ?aya daga cikinsu, babu ranar da zata zo ta wuce bamu yi waya da kowanensu ba saboda a siyasa kana tafiya ne da mutanen da kuke da ra’ayi iri ?aya.”
“Muna da wani ra’ayi da yazo ?aya, sun san cewa na tsani cin amanar jam’iyya, siyasa ta kunshi yaudara da zagon ?asa amma da ka tuna akwai masu goya maka baya sai kaji kamar ka cimma gaci.”
Tun farko, gwamna Wike yace sun kai wannan ziyara ne domin nuna wa abokinsu, gwamnan Bauchi cewa ana tare kuma sun san cewa yana neman tazarce.