Akwai Alaka Tsakanina Da Gwamnoni Biyar Masu Adawa Da Atiku – Gwamna Bala

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, yace akwai wani abu da ya haɗasu inuwa ɗaya da gwamnonin tawagar G5 karkashin jagorancin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Tawagar G5 ta ƙunshi Wike, Samuel Ortom na jihar Benuwai, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ipeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, dukkansu basu ga maciji da ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

“Gwamnonin G5 kamar yadda suka raɗa wa kansu sun kira kansu da ‘Tawagar gaskiya’. Kamata ya yi ace ina tare da su amma basu neme ni ba saboda wani dalili da su kaɗai suka sani.” “Amma ina da alaƙa mai ƙarfi da su, kowane ɗaya daga cikinsu, babu ranar da zata zo ta wuce bamu yi waya da kowanensu ba saboda a siyasa kana tafiya ne da mutanen da kuke da ra’ayi iri ɗaya.”

“Muna da wani ra’ayi da yazo ɗaya, sun san cewa na tsani cin amanar jam’iyya, siyasa ta kunshi yaudara da zagon ƙasa amma da ka tuna akwai masu goya maka baya sai kaji kamar ka cimma gaci.”

Tun farko, gwamna Wike yace sun kai wannan ziyara ne domin nuna wa abokinsu, gwamnan Bauchi cewa ana tare kuma sun san cewa yana neman tazarce.

Labarai Makamanta

Leave a Reply