Ajiyar Abacha: Kotu Ta Umarci Tinubu Ya Bayyana Adadin Kudin Da Ya Dawo Najeriya

Wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin cewa a bayyana yadda aka kashe ku?a?e da suka kai dala biliyan biyar da ake zargin tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha ya sace amma aka ?wato su tare da mayar wa ?asar.

Bayanai sun ce an mayar wa Najeriya ku?in da ake kira da ‘satar Abacha’ a lokacin mulkin shugabannin ?asar kamar Olusegun Obasanjo da Umar Musa Yar’adua da Goodluck Jonathan da kuma Muhammadu Buhari.

Kotun ta kuma umarci gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bayyana takamaimai yawan ku?in da tsohon shugaban mulkin soji Janar Sani Abacha ya sace wa ?asar da kuma dukkan abin da aka gano tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokra?iyya.

Abacha ya mulki Najeriya, ?asa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka daga 1993 zuwa 1998, lokacin da Allah ya yi masa cikawa.

Kungiyar Transparency International mai fafutukar ya?i da rashawa ta ?iyasta cewa Abacha ya wawure dukiyar al’ummar Najeriya da ta kai dala biliyan biyar, inda ta ce kuma babu wanda ya ta?a gurfanar da shi gaban kotu a kan batun.

Wata ?ungiya mai rajin ya?i da hanci da rashawa a Najeriya SERAP ce ta shigar da ?ara gaban kotun inda bu?aci a tilasta wa gwamnati bayyana ku?a?en almundahanar Abacha.

A tsawon shekaru da suka gabata, Amurka da Switzerland da kuma Birtaniya na cikin ?asashen da suka mayar wa Najeriya ?aruruwan miliyoyin daloli da ke da ala?a da Abacha.

Kotun dai ta bai wa gwamnati umarnin ta fito ta yi bayani dalla-dalla a kan yawan ku?in da Abacha ya sace da kuma yarjejeniyoyin da gwamnatocin Najeriya na baya suka cimma da ?asashen waje don mayar wa ?asar irin wannan dukiya zuwa yanzu.

Kungiyar SERAP wadda ta gabatar da ?ara kan batun, ta rubuta wa shugaba Tinubu wasi?a a ranar Lahadi, inda ta yi kira gare shi da ya bi umarnin kotun.

Related posts

Leave a Comment